Tsohon dan takarar shugaban kasa Peter Obi ya sanar da ficewarsa daga Labour Party tare da komawa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC). Ya bayyana cewa wannan mataki ne na dabarar siyasa domin ci gaba da burinsa na ganin Najeriya ta samu sabuwar tafiya ta ci gaba da adalci.
A cikin sanarwar da ya fitar, Obi ya ce Najeriya ta kai wani mataki mai mahimmanci da ke bukatar jagoranci mai hangen nesa, hadin kai da tsayin daka wajen magance kalubalen kasa. Ya jaddada bukatar karfafa dimokuradiyya, ingantacciyar zabe, gaskiya da rikon amana a shugabanci, tare da yin garambawul ga tsarin zabe domin tabbatar da sahihanci da gaskiya.
Obi ya ce duk da matsalolin kasa, yana da yakinin cewa Najeriya na da damar tashi ta hanyar jagoranci nagari, tsari mai kyau da hadin kan jama’a. Ya ce tafiyarsa ta siyasa ta zame masa darasi, tare da burinsa na ci gaba da aiki tare da masu tunani iri daya a cikin ADC domin ci gaban kasa, hadin kai da ingantaccen shugabanci.














