Kasar India ta karɓi shugabancin kungiyar BRICS na shekarar 2026, inda ake sa ran za ta mayar da hankali kan ci gaba mai haɗa kowa da kare muradin kasashe masu tasowa. Wannan ya zo ne a dai-dai lokacin da sabon tsarin harajin Shugaba Donald Trump ke kara haifar da tashin hankali a harkokin kasuwanci.
Kungiyar BRICS, wacce ta fara da Brazil, Russia, India, China da South Africa, yanzu ta faɗaɗa da ƙasashe kamar Egypt, Ethiopia, Indonesia, Iran da UAE, yayin da Saudi Arabiya ke kan hanya. A halin yanzu, BRICS na wakiltar kusan 49% na al’ummar duniya, tare da kusan 29% na GDP da 23% na cinikayyar duniya.
Dangantakar kasuwanci tsakanin India da Amurka ta yi tsami bayan Trump ya kakaba harajin 50% kan kayayyakin India, tare da ƙarin 25% saboda sayen danyen man Rasha. Duk da matsin lamba, masana sun ce India za ta guji takaddama kan batun sabuwar kudin BRICS, maimakon haka ta inganta biyan kasuwanci da kudaden ƙasashe kai tsaye domin kare ’yancin tsarinta.
Masana sun ce India za ta:
ƙara ƙaimi a kan gyaran WTO da IMF,
kare tsarin kasuwanci na ƙasa da ƙasa,
ƙara dagewa a kan muradin Global South, ciki har da batun yunwa, hauhawar farashin man fetur, bashi da kuɗin kare muhalli.
A lokaci guda kuma, ana sa ran India za ta nemi a samar da tsayayyun ƙa’idoji kan sabbin shigowa BRICS domin kada faɗaɗawa ta lalata tasirin kungiyar.














