A wani sabon jawabi da ke nuni da tsananta matsin lamba a yankin Latin Amurka, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargaɗi mai tsauri ga shugaban Colombia Gustavo Petro, yana zarginsa da kasancewa cikin gaba wajen samar da miyagun ƙwayoyi da safarar su zuwa Amurka, kuma ya ce dole ya kiyayi kansa.
Trump ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani kan kalaman Petro game da hare-haren da Amurka ta kai Venezuela tare da kama tsohon Shugaban ƙasar Nicolas Maduro da fitar da shi daga ƙasar.
Trump ya kara da cewa kafin wannan farmaki, ya sha bayyana zargin cewa Venezuela na taka rawa wajen shigar da miyagun ƙwayoyi cikin Amurka, abin da ya ce ya zama ɗaya daga cikin dalilan daukar matakin soja domin dakile barazanar da ta dade tana damun yankin.
Baya ga Colombia, Trump ya kuma jawo hankalin Cuba, yana bayyana ƙasar a matsayin wadda ta gaza, tare da dorawa shugabanninta alhakin matsin tattalin arziki da jama’arta ke fama da shi tsawon shekaru. Ya ce ba da jimawa ba Amurka za ta waiwayi Cuba domin daukar sabbin matakai, yana jaddada cewa Washington na son taimaka wa al’ummar Cuba da kuma wadanda aka tilasta musu barin ƙasarsu.














