Wani kifi mai nauyin kusan kilogiram 243 ya ja hankalin duniya bayan an sayar da shi kan kuɗi har dala miliyan 3.2, kwatankwacin Naira biliyan 4.5, a gwanjon farko na shekara da aka gudanar a kasuwar kifaye ta Toyosu a birnin Tokyo na ƙasar Japan.
An kama kifin nau’in bluefin tuna ne a gabar tekun Oma da ke arewa maso gabashin Japan, yayin da kamfanin Kiyomura Corp, mallakin sarkar gidajen abinci na Sushizanmai, ya mallake shi. Shugaban kamfanin, Kiyoshi Kimura, ya bayyana cewa sayen kifin na farko a shekarar na da alamar sa’a, inda ya ce suna fatan mutane da dama za su amfana da cin kifin.
Kamfanin ya sanar da cewa za a yayyanka kifin ne a reshen Sushizanmai da ke Tsukiji, sannan a raba shi zuwa sauran rassan kantin a faɗin Japan. Duk da tsadar kuɗin da aka kashe wajen sayensa, Kiyomura ya tabbatar da cewa za a sayar da kifin ga jama’a a farashin da aka saba.
Hukumar kula da birnin Tokyo ta bayyana cewa wannan shi ne mafi tsadar kifi da aka taɓa saye tun bayan fara adana bayanan gwanjon kifaye a shekarar 1999. Masu saye kan kashe makuɗan kuɗi a irin wannan gwanjo saboda imanin cewa sayen kifi a farkon shekara na kawo sa’a da bunƙasar kasuwanci.
Gwanjon ya kuma jawo hankalin masu yawon buɗe ido daga ƙasashen waje, waɗanda suka halarta domin shaida bikin da ake gudanarwa a duk farkon shekara, lamarin da ke ƙara wa kasuwar armashi.














