Jami’an ‘yan sanda sun gano wani bam da bai fashe ba a kauyen Zugurma na Mashegu, lamarin da ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin kafin daga bisani hukumomin tsaro su ɗauki matakin gaggawa. Wannan na zuwa ne sakamakon bayanan sirri da aka samu daga al’umma.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa an gano nakiyar ne bayan rahoton da jami’in yankin Ibbi ya bayar a ranar Litinin. Ya ce mazauna yankin sun ga wani abin da ake zargin bam ne a cikin daji, lamarin da ya sa aka hanzarta tura jami’ai zuwa wurin domin kare rayukan jama’a.
Bayan killace yankin, kwamishinan ‘yan sanda Adamu Elleman ya umarci sashen kwance bamabamai karkashin jagorancin CSP Mohammed Mamun da su isa wurin. Rahotanni sun tabbatar da cewa tawagar ta samu jagorancin al’ummar yankin zuwa wurin da aka boye bam ɗin, inda daga bisani aka kwance shi cikin nasara tare da kai shi hedikwata a Minna.
Rundunar ta ce an fara bincike domin gano asalin bam ɗin da yadda ya riski yankin, tare da alƙawarin fitar da karin bayani a nan gaba. Haka kuma kwamishinan ‘yan sanda ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, yana mai tabbatar da cewa hukumomin tsaro suna nan kan bakin aikinsu na kare rayuka da tabbatar da zaman lafiya.














