Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin wucin gadi na kwace kadarori guda 57 da ake dangantawa da tsohon Ministan Shari’a na Tarayyar Najeriya, Abubakar Malami (SAN), tare da wasu ‘ya’yansa biyu.
Kotun ta bayyana cewa kadarorin, wadanda kimar su ta kai ₦213,234,120,000, ana zargin an samo su ne ta hanyar da ba ta dace ba, kuma suna cikin Abuja, Kebbi, Kano da Kaduna. Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da wannan umarni bayan wani ƙarar gaggawa da Lauyan EFCC, SAN Ekele Iheanacho, ya shigar a gaban kotu.
A cikin hukuncinsa, mai shari’ar ya ce kadarorin za a mika su na wucin gadi ga Gwamnatin Tarayya, tare da bayar da umarni a wallafa sanarwar a jarida domin ba duk wanda ke da bukatar su damar bayyana hujja cikin kwanaki 14. An dage shari’ar zuwa 27 ga Janairu, 2026 domin ci gaba da sauraro da kuma bayar da rahoton bin umarni. A halin yanzu, Malami, matarsa da ɗansa na fuskantar shari’ar zargin halatta kuɗin haramun da yawansu ya kai ₦8.7bn a gaban kotun.














