Rahoton Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ya nuna cewa kamfanonin rabon wutar lantarki a Najeriya (DisCos) sun samu ƙaruwar kudin shiga a zangon uku na shekarar 2025, sakamakon ci gaba da tallafin gwamnati duk da hauhawar kudin samar da wuta. Gwamnatin Tarayya ta biya tallafin wutar lantarki na kimanin ₦458.75 biliyan a cikin watanni uku, yayin da hukuma ta ce tsarin daskarar da wasu farashin wuta tun watan Yuli 2024 ya kara nauyi ga gwamnati duk da ƙarin kuɗin samar da wutar.
A cewar rahoton, karfin tattara kudin biyan wuta ya kai kashi 80.7%, inda aka tara ₦570.21 biliyan daga cikin ₦706.61 biliyan da aka lissafa wa kwastomomi tsakanin Yuli zuwa Satumba 2025. Duk da gabatar da tsarin Band A, NERC ta ce tallafin gwamnati ya ci gaba da zama ginshiki wajen tabbatar da dorewar sarkar samar da wutar lantarki, inda ya rufe kusan kashi 58.63% na kuɗaɗen kamfanonin samar da wuta (GenCos) a lokacin rahoton.
Rahoton ya bayyana cewa jimillar kudin wutar da DisCos suka karɓa ta kai ₦854.53 biliyan, yayin da billing efficiency ya kai 82.69%. Duk da haka, an samu asarar lissafin kudade na ₦147.92 biliyan, sai dai collection efficiency ta karu zuwa 80.7% idan aka kwatanta da zangon baya. NERC ta jaddada cewa gwamnatin tarayya tana cike gibin farashi tsakanin farashin da ya dace da hakikanin kudin samarwa da kuma abin da ke kan takarda ta hanyar tallafi ga kasuwar wuta.
Rahoton ya kuma nuna raguwar tallafin gwamnatin tarayya idan aka kwatanta da zangon baya, tare da bayyana cewa raguwar ƙarfin sayen wuta daga DisCos da raguwa a ainihin kudin samar da kWh sun taka rawa. Haka kuma, ya fito da bambance-bambancen aiki tsakanin DisCos, inda Ikeja Disco ta samu mafi girman nasarar tattara kudade (100%), yayin da Kaduna Disco ta kasance mafi ƙasa da kashi 45.67%.














