Gabas Ta Tsakiya Zaman Lafiya

YPG Ta Kwace Asibiti a Aleppo, Ta Kori Ma’aikatan Lafiya

Kungiyar YPG ta kwace wani asibiti a unguwar Sheikh Maqsoud ta Aleppo tare da korar ma’aikatan lafiya, lamarin da ya janyo damuwa kan tsaron fararen hula.

Newstimehub

Newstimehub

10 Jan, 2026

328e52ab13866b5c57588d5a9e9f332bce20c6109a61d2ebcf40df96b329cc78

Rahotanni daga Syria sun nuna cewa kungiyar YPG ta kwace iko da Asibitin Yassin da ke unguwar Sheikh Maqsoud a birnin Aleppo, inda ta kori likitoci da sauran ma’aikatan lafiya tare da mayar da asibitin sansanin soja.

Ma’aikatar Lafiya ta Syria, a wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasar SANA ya wallafa, ta ce ‘yan kungiyar PKK da ke da alaƙa da YPG sun tilasta wa ma’aikatan asibitin ficewa bayan sun tsere gaban Rundunar Sojan Syria. Hukumomin sun gargadi fararen hula da su nisanci yankin saboda barazanar tsaro.

A wani bangare, majiyoyin soji sun ce wani ɗan kungiyar YPG ya kai harin kunar-baƙin-wake kusa da rundunar soji a Sheikh Maqsoud, amma ba a samu asarar rai ba. Rundunar Sojan Syria ta bayyana cewa ta kammala share yankin tare da tabbatar da tsaro.

Hare-haren da aka ce kungiyar YPG ta kai a unguwannin Aleppo sun kashe mutane tara, sun jikkata fiye da 50, tare da tilasta wa dubban mazauna yankin barin gidajensu. Hukumomi sun ce duk da yarjejeniyar da aka kulla a watan Maris domin haɗa ƙungiyar cikin hukumomin gwamnati, YPG ba ta cika sharuddan da aka amince da su ba.

Majiyar Labari: TRT HAUSA