Birnin Minneapolis na Amurka ya sake fuskantar zanga-zanga mai zafi ranar Juma’a, karo na uku a jere, sakamakon mutuwar wata uwa ’yar shekara 37 da jami’in hukumar shige da fice ta ICE ya harba a yayin wani aiki.
Marigayiyar, Renee Nicole Good, uwa ce ga yara uku, wadda aka kashe a ranar Laraba yayin da take zaune a cikin motarta lokacin da jami’in ICE ya buɗe wuta. Lamarin ya tayar da hankalin al’umma tare da haifar da fushin jama’a a faɗin ƙasar.
Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka (DHS) ta ce harbin ya faru ne a matsayin kare kai, inda ta zargi marigayiyar da yunƙurin tare jami’ai tare da ƙoƙarin amfani da motarta wajen cutar da su. Sai dai masu zanga-zanga sun yi watsi da wannan bayani, suna kiran lamarin da cin zarafin iko.
A zanga-zangar ranar Juma’a a tsakiyar birnin, jama’a sun rike alluna da tutoci suna neman adalci, yayin da ’yan sanda suka ayyana taron a matsayin wanda ya saɓa doka, lamarin da ya kai ga kama mutane da dama.
Gwamnatin Minnesota ta ce jami’an tsaro na jiha sun shiga tsakani domin tarwatsa taron, yayin da wasu masu zanga-zangar suka durƙusa a ƙasa domin nuna alhini da adawa.
A halin yanzu, gwamnatin Shugaba Donald Trump ta tura kusan jami’ai 2,000 daga ICE da FBI zuwa Minneapolis, matakin da ya ƙara hura wutar suka da adawa daga jama’a da kungiyoyin kare haƙƙin ɗan-adam.
An kuma ruwaito irin wannan zanga-zanga da zaman makoki a wasu biranen Amurka, yayin da ake ci gaba da kira ga hukuma da ta ɗauki alhakin mutuwar Renee Nicole Good.














