Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa duk wata ƙasa da ke ci gaba da hulɗar kasuwanci da Iran za ta fuskanci harajin kashi 25 cikin 100 kan duk wata mu’amala da za ta yi da Amurka, inda ya ce matakin zai fara aiki nan take ba tare da wata togaciya ba.
A cikin sanarwar da ya fitar, Trump ya jaddada cewa hukuncin zai shafi kowace ƙasa da ta ki dakatar da kasuwanci da Tehran, yana mai cewa duk wata hulɗa da Washington za ta kasance ƙarƙashin sabon tsarin haraji.
Shugaban ya sake nanata barazanar a wasu sanarwa, yana bayyana cewa manufarsa ita ce ƙara matsin lambar tattalin arziki ga Iran ta hanyar danganta damar shiga kasuwar Amurka da bin ƙa’idojin cinikayya da suka shafi hulɗa da ƙasar.














