Gwamnatin Turkiyya ta yi gargaɗin cewa tsoma bakin ƙasashen waje a rikicin da ke ƙara kamari a Iran zai iya haddasa babbar barazana ga zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya. Mataimakin shugaban Jam’iyyar AK kuma kakakinta, Omer Celik, ya ce Ankara ba ta goyon bayan rikici a maƙwabciyarta Iran, tana mai jaddada cewa ya kamata a magance matsalolin ƙasar ta hanyar tattaunawa da hanyoyin cikin gida.
Celik ya bayyana cewa shiga tsakani daga waje, musamman daga Isra’ila, na iya janyo rashin kwanciyar hankali mai tsanani a yankin. Ya ƙara da cewa kalaman barazana da ake yi na iya rura wutar rikici, yana mai kira da a fifita sulhu da mutunta ikon Iran na warware matsalolinta.
Wannan gargaɗin ya zo ne a daidai lokacin da Iran ke fuskantar manyan zanga-zanga, yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna yiwuwar shiga tsakani, lamarin da ke ƙara tayar da hankalin kasashen yankin.














