Sojojin Sudan sun yi nasarar daƙile wani hari da rundunar Rapid Support Forces (RSF) tare da abokiyarta SPLM-North suka kai a garin Al-Kuweik da ke jihar Kudancin Kordofan, kamar yadda majiyoyin soji suka tabbatar. An ce harin ya faru ne da sassafe, amma dakarun gwamnati sun yi gaggawar mayar da martani, inda aka tilasta wa maharan janyewa bayan fafatawa mai zafi.
Majiyoyin sun ce sojoji sun kwace motoci masu sulke da kayan yaƙi daga hannun RSF a yayin artabun, lamarin da ya janyo murna a cikin sansanonin sojoji. Har yanzu RSF da SPLM-North ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.
A ‘yan makonnin nan, jihohin Kordofan uku – Arewa, Yamma da Kudu – sun kasance cikin rikici mai tsanani, wanda ya tilasta dubban fararen hula tserewa daga gidajensu. Rikicin da ke tsakanin sojojin Sudan da RSF tun daga Afrilun 2023 ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da jefa miliyoyi cikin gudun hijira.














