A daren Talata ne wata gobara ta tashi a wani gidan mai da ke Rimin Kebe, ƙaramar hukumar Nassarawa a jihar Kano, lamarin da ya janyo asarar dukiya mai yawa, ciki har da Adaidaita Sahu 16 da tankokin dakon mai guda biyu.
A cewar kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, gobarar ta samo asali ne yayin da wani tankar mai ke sauke man fetur a gidan man, inda wutar ta bazu cikin gaggawa ta kama motocin Adaidaita da ke kusa da wurin.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce jami’anta sun kai ɗauki da gaggawa domin shawo kan wutar, kuma babu rahoton asarar rayuka a yayin aukuwar lamarin. Daraktan hukumar, Sani Anas, ya shawarci masu gidajen mai da direbobin tankoki da su bi ƙa’idojin tsaro yadda ya kamata a lokacin sauke mai.
Ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su rika sanar da duk wata gobara cikin gaggawa ta layukan gaggawa na hukumar, domin rage asarar rayuka da dukiya.














