Gwamnatin Kamaru ta tabbatar da cewa ‘yan ta’adda sun kashe mutane 14, ciki har da yara bakwai, a wani mummunan hari da suka kai a ƙauyen Guidado da ke yankin arewa maso yammacin ƙasar, inda ake magana da Turancin Ingila.
A cewar rahoton gidan talabijin na gwamnati CRTV, gwamnan yankin, Adolphe Lele Lafrique, ya bayyana cewa harin ya faru ne da safiyar Talata, inda aka kashe namiji babba guda ɗaya, mata manya shida da kuma yara ƙanana masu shekaru tsakanin biyu zuwa 11.
Gwamnan ya ƙara da cewa an garzaya da wasu mutane 14 da suka jikkata zuwa asibitoci a yankin domin samun kulawar gaggawa. Haka kuma, Shugaba Paul Biya ya bayar da umarnin ɗaukar matakan tsaro domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Yankunan Kamaru masu magana da Turancin Ingila na fama da rikici tun shekaru, inda ‘yan aware masu neman ‘yancin kai ke yawan kai hare-hare, garkuwa da mutane ko kashe ‘yan siyasa, ma’aikatan gwamnati da malaman makaranta da suke zargin suna goyon bayan gwamnati.
Sai dai gwamnatin Kamaru ta sake jaddada matsayinta na cewa ƙasar dunƙulalliya ce, kuma ba za ta amince da duk wani yunkurin raba ƙasa ba.














