Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa ƙasarsa ba ta goyon bayan tsoma bakin ƙasashen waje a cikin rikicin da ke gudana a Iran, yana mai jaddada muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Erdogan ya faɗi hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, inda ya nuna damuwa kan yadda rikicin ke ƙara taɓarɓarewa.
A cewar wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar Turkiyya ta wallafa a shafin X, Erdogan ya ce Turkiyya tana mutunta ‘yancin ƙasashe makwabta kuma tana goyon bayan warware rikice-rikice ta hanyar tattaunawa ba tare da tsoma bakin waje ba.
A halin yanzu, Iran na fuskantar gagarumar zanga-zanga da yajin aiki, mafi tsanani tun bayan juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979. Jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, ya bayyana cewa sama da mutane 7,000 sun rasa rayukansu sakamakon murƙushe masu zanga-zangar, yana zargin Amurka da hannu a rikicin.
Rahotanni sun nuna cewa tattalin arzikin Iran ya shiga mawuyacin hali, lamarin da ya ƙara hura wutar adawa da gwamnatin malaman addini. Zanga-zangar dai ta fara ne tun daga ranar 8 ga Janairu, kuma har yanzu tana ci gaba a manyan biranen ƙasar.
Ministan harkokin wajen Iran ya kuma aika da gargaɗi ga Amurka, yana mai cewa ƙasar za ta mayar da martani da ƙarfi idan aka sake kai mata hari. A wani rahoto na hukumomi, an ce zuwa ranar Laraba, mutane 3,117 ne aka tabbatar sun mutu yayin rikicin.














