Afirka Zaman Lafiya

Ba Zaman Lafiya a Sudan Sai an Kawar da RSF – Burhan

Shugaban Sudan Burhan ya ce ba za a samu zaman lafiya ba sai RSF ta miƙa makamanta, yana mai cewa duk wata sulhu da ta bar su da ƙarfi ba za ta kawo ƙarshen yaƙi ba.

Newstimehub

Newstimehub

26 Jan, 2026

4aced0ae6b14223fd0a85b817c826a59c8d2b0ca13b2cc090f962bcee8b58e9d

Shugaban gwamnatin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya bayyana cewa ba za a taɓa samun zaman lafiya na gaskiya a ƙasar ba muddin rundunar kai ɗaukin gaggawa ta RSF na ci gaba da wanzuwa da makamai. A cewarsa, duk wata tattaunawar sulhu da ta bar RSF cikin tsarin tsaro ba za ta kawo ƙarshen yaƙin ba, sai dai jinkirta shi ne kawai.

Burhan ya faɗi haka ne a Port Sudan, inda ya jaddada cewa hanyar samun zaman lafiya mai ɗorewa ita ce RSF ta miƙa makamanta ta yi saranda. Ya ce ba lallai ne a hallaka dakarun ba, amma dole ne a kawar da su a matsayin rundunar makami mai zaman kanta.

Ya kuma zargi RSF da haddasa babbar ɓarna ga fararen hula da gine-gine a faɗin ƙasar, yana mai cewa dukkan al’ummar Sudan sun haɗa kai wajen tsayawa tsayin daka don kare ƙasar.

Game da yunƙurin shiga tsakani, Burhan ya ce Sudan ta amince Turkiyya, Qatar, Saudiyya da Masar su taka rawa a sulhun, amma RSF ta ƙi amincewa. Ya jaddada cewa sojojin Sudan ba su daidaita da RSF a ƙarfi da halacci, yana mai cewa duniya ma ta san haka.

Tun Afrilu 2023, Sudan na cikin yaƙin basasa bayan rikici ya ɓarke kan batun haɗa RSF da rundunar sojin ƙasa, rikicin da ya jawo mummunar masifar jinƙai, mutuwar dubban mutane da raba miliyoyi da muhallansu.

Majiyar Labari: TRT HAUSA