Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ta sanar da amincewa da shirin tsagaita wuta da Angola ta gabatar tsakanin gwamnati da ƙungiyar ‘yan tawaye ta AFC/M23. Sanarwar daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana matakin a matsayin wani ci gaba mai muhimmanci a kokarin kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe yana addabar gabashin ƙasar.
Shirin, wanda Shugaban Angola Joao Lourenco ya gabatar, na tanadin fara tsagaita wuta daga 18 ga Fabrairu. Hakan ya biyo bayan ganawar da aka yi a Luanda tare da Shugaban Congo Felix Tshisekedi, Shugaban Togo Faure Gnassingbe, da Olusegun Obasanjo, ɗaya daga cikin masu sasanci na AU.
Gwamnatin Congo ta ce an amince da tsagaita wutar ne domin samar da mafita ta lumana, tare da gargadin cewa duk wani yunƙuri na sauya matsayin soji a wannan lokaci zai iya lalata amincin tattaunawar. Har yanzu babu martani kai tsaye daga AFC/M23.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce rundunar MONUSCO za ta tura dakarunta zuwa Uvira domin sa ido kan tsagaita wutar idan an cika sharuddan tsaro. M23 na ci gaba da kasancewa muhimmin ɓangare na rikicin, inda ke rike da manyan yankuna ciki har da Goma da Bukavu.
Majiyar Labari: TRT AFRIKA














