Kotun tafi-da-gidanka da ke Bolade-Oshodi ta gurfanar da mutane 17 da jami’an Lagos Waste Management Authority (LAWMA) suka kama suna yin fitsari da bahaya a wuraren jama’a.
Sanarwar ta fito ne daga Tokunbo Wahab, Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa na Jihar Lagos, ta shafinsa na X. Ya ce an same su da laifi kuma an yanke musu hukuncin daurin wata guda, tare da zabin biyan tara.
Ya kuma jaddada cewa yin bahaya da fitsari a fili barazana ce ga lafiyar jama’a, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da kakaba dokokin muhalli domin tabbatar da tsafta da kare mutunci.
Majiyar Labari: TVC NEWS














