Lebanon ta zargi Isra’ila da shirin mamaye ko kwace wasu yankuna a kudancin kasar, bayan Firayim Minista Nawaf Salam ya shaida wa Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres cewa kalaman wasu manyan jami’an Isra’ila da hare-haren da ake kaiwa a yankin suna barazana ga ikon mallakar kasar. Rahotannin hukuma sun ce Salam ya danganta wannan zargi da kalaman da suka yi magana kan mamaye yankin kudancin kogin Litani ko ma haɗa shi da Isra’ila.
A cewarsa, hare-haren ba wai a kan sojoji kaɗai suka tsaya ba, domin an lalata manyan gadojin da ke kan kogin Litani, an tilasta wa mutane da yawa barin gidajensu, sannan ana ci gaba da kutse da rusa gidaje a wasu garuruwa. Salam ya yi gargadin cewa irin wannan yanayi na iya hana fararen hula komawa gidajensu nan gaba kusa, abin da Lebanon ke kallon sa a matsayin babbar barazana ga yankinta da haƙƙin jama’arta.
Lebanon ta kuma ce za ta kai koke kai tsaye gaban Kwamitin Tsaro na MDD, tana neman a dauki mataki domin dakatar da abin da ta kira take dokokin ƙasa da ƙasa da dokokin jin ƙai. Wannan na zuwa ne a lokacin da rikicin ke ƙara tsananta a kudancin Lebanon, bayan kalaman Ministan Kudin Isra’ila Bezalel Smotrich na cewa sabon iyakar Isra’ila ya kamata ya kai kogin Litani, kalaman da suka tayar da hankali a yankin.
Majiyar Labari: AA














