Gabas Ta Tsakiya

Trump ya dakatar da ‘Aikin ‘Yanci’ a Mashigar Hormuz yayin da aka ci gaba da tattaunawa da Iran

Shugaban Amurka ya ce Washington za ta dakatar da ayyukanta na wucengadi yayin da take ci gaba da yi wa Iran ƙawanya, yana mai iƙirarin cewa “an samu gagarumar ci-gaba wajen samun cikakkiyar yarjejeniya ta ƙarshe da wakilan Iran.”

Newstimehub

Newstimehub

6 May, 2026

2026 05 05t165905z 1 lynxmpem4413q rtroptp 3 usa trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shi zai dakatar da ayyukan sojin Amurka na raka jiragen ruwa ta mashigin ruwan Hormuz bayan kwana ɗaya kawai , a wani mataki na kai ga yarjejeniya da Iran domin kawo ƙarshen yaƙin Gabas Ta Tsakiya .

“Aikin ‘Yanci (Tafiyar jiragen ruwa ta mashigin ruwan Hormuz) za a dakatar da shi na ƙaramin lokaci domin ganin ko za a iya tabbatar da yarjejeniya da kuma rattaɓa hannu a kanta ko kuma hakan ba zai yiwu ba ,” kamar yadda Trump ya bayyana a shafin sada zumuntansa na Truth Social.

Yayin da yake ishara ga kiraye-kiraye daga Pakistan da sauran ƙasashe, tare da ci-gaban da aka samu na cim ma yarjejeniya ta ƙarshe da Tehran, Trump ya yi shelar hukunci na baya bayan nan da aka yanke, amma ya haƙiƙance cewa ƙawanya ta sojin ruwa za ta ci gaba da aiki.

Daga farko dai a yau, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce matakin yaƙi da Amurka ta ƙaddamar kan Iran a watan Fabrairu ya ƙare kuma a yanzu Amurka ta mayar da hankali ne kan wani sabon aiki na raka jiragen ruwa ta mashigin ruwan Hormuz.

Yiyuwar samun yarjejeniya da Iran

A ranar Litinin ne Trump ya yi shelar “Aikin ‘Yanci”, kuma ana tsammanin aikin zai taimaka wa jirage ruwa daga ƙasahen da ba sa cikin yaƙin da Iran su iya wucewa cikin aminci ta mashigin ruwan Hormuz.

Aikin da hedikwatar soji ta tsakiyar Amurka (CENTCOM) ke yi ya ƙunshi na’urori masu lalata makamai masu linzami da jiragen sama fiye da 100, da kafofi mara matuƙa da kuma dubban ma’aikata da ke ba da jagoranci da kauce wa nakiya da kuma kasancewa cikin shiri na kare jiragen ruwa na ‘yan kasuwa da ba su da cikakkun ‘yan rakiya.

An yi shirin ne domin warware toshe mashigin da Iran ta yi inda ta katse gudanar mai a duniya kuma kuma an bayyana shi ne a matsayin wani taƙaitaccen mataki na kariya da ya mayar da hankali kan ‘yancin tafiya ta ruwa da kuma kare tafiyar jiragen ruwa da ba su ji ba ba su gani ba.

Aikin dai ya fuskanci tsaiko daga farko inda aka yi muasayar wuta, amma yanzu an dakatar da shi domin ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya domin yiyuwar samun yarjejeniya da Iran.