Nijeriya

‘Yanbindiga sun kashe aƙalla mutum 20 Jihar Kebbi ta Nijeriya

Hukumomi sun yi Allah wadai da kashe-kashen kuma sun sha alwashin ɗaukar matakan tsaro yayin da hare-haren ƙungiyoyin ‘yanbindiga ke ƙaruwa.

Newstimehub

Newstimehub

16 Jun, 2026

2026 03 17t170911z 1977050511 rc2mnia28mcm rtrmadp 3 nigeria security militants

Aƙalla mutum 20 ne aka kashe lokacin da mayaƙan Lakurawa suka kai hari ƙauyen Fasken Rafi a ƙaramar hukumar Arewa a jihar Kebbi a arewa maso yammacin Nijeriya, kamar yadda kafafan watsa labarai na ƙasar suka ruwaito.

Harin na ranar Lahadi da mazauna wurin suka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin hare-hare da aka tsara sosai a kan al’ummar a ‘yan kwanakinnan ya kuma raunata wasu mutane, inda waɗanda lamarin ya rutsa da su ke karɓar magani a cibiyoyin lafiyar da ke kusa.

Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da aukuwar lamarin kuma ta tura wata tawaga a ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Umar Tafida ga al’ummar da lamarin ya rutsa da su domin nazari da kuma tattaunawa da iyalan waɗanda harin ya rutsa da su.

Da yake magana a lokacin ziyarar, Tafida ya yi Allah wadai da kashe-kashen kuma ya sha alwashin ƙarfafa matakan tsaro.

“Wannan rasa rayukan mara dalili ya baƙanta mana rai matuƙa. Wannan gwamnatin ta tsaya tsayin daka a jajircewarta domin dawo da zaman lafiya ,” kamar yadda ya faɗa, yana mai ƙarawa da cewa za a ƙara tura ƙarin jami’an tsaro da kayayyakin aiki zuwa yankin.

Damuwa a kan yanayin tsaro ta ƙaru a faɗin arewa maso yammacin Nijeriya, inda al’ummomi ke fuskantar hare-hare daga ƙungiyoyin ‘yanbindiga ciki har da masu tayar da ‘yan Lakurawa, waɗanda suka faɗaɗa aika-aikarsu a yankunan jihar Kebbi da jihar Sokoto mai maƙwabtaka.

Harin ya zo ne kwanaki bayan Sarkin Argungu, Mohammed Mera, ya yi kira ga al’ummomi su duba batun matakan kare kai da suka dace da doka, ciki har da samun lasisin riƙe bindigogi, yayain da ƙungiyoyin ‘yan bindiga ke kai musu hare-hare.

Yankin Arewa na jihar Kebbi ya fuskanci wasu hare-hare masu muni a cikin ‘yan watannin nan.

A watan Fabrairu, fiye da mutum 30 ne aka kashe a lokacin da masu tayar da ƙayar baya na Lakurawa suka ƙaddamar da hare-hare kan ƙauyuka a ƙaramar hukumar.

Ƙungiyar Lakurawa ta fito ne a arewa maso yammacin Nijeriya a cikin ‘yan shekaraun nan, tana mai amfani da kan iyaka tsakanin Nijeriya da Nijar domin samun gindin zama a cikin alummomin.

Daga farko ta fara ne da bayyana kanta a matsayin ƙungiyar jaddada addini da kuma ba da tsaro a ƙauyuka, amma ana yawan alaƙanta ƙungiyar da hare-hare da ƙwace da satar shanu da ƙaƙaba dokokin aƙidoji masu tsauri.

Hukumomin Nijeriya sun ayyana Lakurawa a matsayin ƙungiyar ta’addanci a shekarar 2024 kuma tuni suka zafafa kai samame kan mayaƙan, waɗanda aka yi imanin cewa suna da alaƙa da ƙungiyoyin ‘yanta’adda a faɗin yankin Sahel.