Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Kwamitin Zaman Lafiya na Gaza ya cim ma yarjejeniya kan ajiye makamai na Hamas da duk ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a Gaza da aka killace, wadda za a aiwatar da ita cikin matakai daban-daban.
Kazalika hakan zai sa sojojin mamaya na Isra’ila su fice daga yankin Falasɗinawa.
“A yau, Kwamitin Zaman Lafiya ya cim ma yarjejeniyar mai cike da TARIHI don KAMMALA KAWAR DA MAKAMAI daga hannun Hamas da sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a Gaza,” kamar yadda Trump ya bayyana a saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social a yammacin Alhamis.
“Wannan babban mataki ne zuwa ga ɗorewar zaman lafiya da tsaro,” in ji Trump.
Shugaban na Amurka ya kuma ce rundunar wanzar da zaman lafiya ta ƙasa da ƙasa za ta yi aiki tare da sabuwar rundunar ‘yansandan Falasɗinawa don kula da tsaron Gaza.
“Yarjejeniyar muhimmin mataki ne zuwa ga kafa sabuwar gwamnatin Falasɗinawa da za ta jagoranci Gaza,” in ji Trump, yana mai gode wa Masar da Qatar da kuma Turkiyya kan ƙoƙarin shiga tsakani da taimakawa wajen tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya.
“Ina so na gode wa masu shiga tsakani – Masar da Qatar da kuma Turkiyya – saboda gagarumin ƙoƙarin da suka yi, musamman tawagata wadda ta taka muhimmiyar rawa da jajircewa wajen aiwatar da wannan gagarumin ci-gaba.”
“A ƙarƙashin wannan yarjejeniya, Gaza za ta kasance a hannun sabuwar gwamnatin Falasɗinawa wadda za ta yi wa al’ummarta hidima,” in ji Trump.
Martanin Hamas
Wani babban jami’in Hamas ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa yarjejeniyar da aka cim ma da Isra’ila ta haɗa da tanade-tanaden da suka shafi makaman ƙungiyar da kuma janye sojojin Isra’ila a hankali daga Gaza.
“An cimma yarjejeniya game da batun makamai.
Haka kuma, an cim ma yarjejeniya kan janyewar (sojojin Isra’ila) a hankali” daga Gaza, in ji wani jami’in Hamas, yana mai ƙara da cewa yanzu ƙungiyar masu fafutukar kare yancin Falasɗinawa tana sa ran masu shiga tsakani da Hukumar Zaman Lafiya za su tabbatar da cewa Isra’ila ta bi ƙa’idodin yarjejeniyar.
Duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cim ma wadda ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoban 2025, Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a kowace rana a faɗin Gaza, inda ta kashe Falasɗinawa 1,214 tare da jikkata wasu 3,977, kuma yawancinsu mata da yara ne, yayin da take ci gaba da haifar da barna masu yawa.
Isra’ila ta ƙaddamar da kisan kare dangi a Gaza a ranar 8 ga Oktoba na 2023, inda ta kashe Falasɗinawa fiye da 73,000 tare da jikkata mutum fiye da 174,000 waɗanda yawancinsu mata da yara ne, yayin da ta lalata kusan kashi 90 cikin 100 na kayayyakin more rayuwa na yankin, kuma duk wannan da oyon bayan jami’an sojojin Amurka da na siyasa.
Masu sharhi sun ce adadin waɗanda suka mutu da jami’an Falasɗinawa suka tattata bayanan su ba a ƙidaya su sosai ba, inda ainihin adadin zai iya ninka sau biyu zuwa uku fiye da kiyasin da ake da shi a yanzu.
A watan Nuwamba, 2024, Kotun Hukunta Manya Laifuka ta Duniya (ICC) ta bayar da sammacin kama Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, tana mai zarginsa da bayar da umarnin “aikata laifukan yaƙi da cin zarafin bil’adama” a Gaza, wanda Isra’ila ta yi wa ƙawanya ta ƙasa da sama da kuma ta teku tun 2005.
An cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a ƙarƙashin shirin Trump mai matakai 20 kan Gaza, na Hukumar Zaman Lafiya, wacce Trump ke jagoranta take kula da shi.
Har yanzu dai babu tabbas kan ko Isra’ila za ta daina keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cim ma bayan sanarwar Trump.
Ana sa ran, Masar za ta karbi bakuncin masu shiga tsakani kan tsagaita wutar Gaza, ciki har da Turkiyya da Amurka da kuma Qatar, kamar yadda kafar Al-Qahera News ta ruwaito.
Kamfanin dillancin labarai, wanda ke da alaƙa da hukumomin leƙen asiri na gwamnati da ke sa ido kan tattaunawar Gaza, bai fayyace lokacin da za a yi taron ba, amma ya ce da safiyar Juma’a zai tattauna kan aiwatar da mataki na biyu na shirin tsagaita wutar Gaza da taswirar da Hamas da ƙungiyoyin Falasdinawa suka amince da ita.
















