Kwamitin gudanarwa na kamfanin Volkswagen ya amince da wani shiri na sake rage ma’aikata 50,000 a faɗin duniya, a matsayin wani ɓangare na babban shirin sake fasalin kamfanin har zuwa shekarar 2030. Wannan raguwar ma’aikatan ƙari ce a kan shirye-shiryen da tuni ake aiwatarwa.
Tun daga ƙarshen shekarar 2024, Volkswagen ya riga ya amince da rage ma’aikatantsa da kusan 50,000 kafin ƙarshen wannan shekaru goma. A kowane mataki na rage ma’aikatan za a rage jumullar ma’aikata 100,000.
Babban Daraktan kamfanin, Oliver Blume, ya bayyana zaɓen da aka yi a Wolfsburg a matsayin “saƙo mai ƙarfi ga makomar Kamfanin Volkswagen,” yana mai cewa Future Plan 2030 shi ne “shirin sauya fasali mafi zurfi a fannin dabarun gudanarwa a tarihin Kamfanin Volkswagen.”
“Mun ɗauki alhakin dukkan ma’aikatanmu, abokan hulɗarmu da kuma ayyukan masana’antu a faɗin duniya,” in ji Blume.
Ya ƙara da cewa, “A cikin shekaru masu zuwa, za mu zuba jarin kuɗi da ya kai ɗaruruwan biliyoyin kuɗi domin ƙara wa shahararrun samfuranmu kyan gani, ƙarfafa su da kuma ƙara musu ƙarfin gasa a kasuwa.”
Kamfanin ya ce ƙara tsanantar gasar duniya, sauyin buƙata da kuma sauye-sauyen fasaha sun sa ya zama wajibi a daidaita yawan ma’aikata da “haƙiƙanin yanayin tattalin arziki.”
A cewar nazarin da aka yi wanda ya samar da wannan shiri, za a buƙaci ƙarin daidaita kusan guraben aiki 50,000 a faɗin rukunin kamfanin, ciki har da guraben ayyukan gudanarwa, baya ga shirye-shiryen da ake da su.
Kamfanin yana ɗaukar ma’aikata kusan 663,000 a faɗin duniya.
Volkswagen ya ce yana da burin sayar da motoci miliyan tara a kowace shekara, wanda ya yi ƙasa da kusan miliyan ɗaya idan aka kwatanta da tsare-tsaren yawan motocin da aka yi a baya, sannan ya yi ƙasa da miliyan uku idan aka kwatanta da kafin ɓullar annobar coronavirus.
Zuwa shekarar 2035, rukunin kamfanin na shirin rage nau’ikan motocinsa da kusan kashi 50 cikin 100 tare da rage sarƙaƙiyar kayayyakin da kusan kashi 75 cikin 100.
Kamfanin ya ce ragowar nau’ikan motocin ya kamata su yi fice wajen ƙira da fasaha, tare da amfana daga ƙarin yawan samarwa da kuma rage kuɗin da ake kashewa wajen kera kowace mota.
Kwamitin ya ce ƙarfin samar da motoci na Kamfanin Volkswagen a Turai a halin yanzu ya fi buƙatar da ake da ita ta fiye da motoci 500,000.
















