Attajirin ɗan kasuwar Nijeriya, Aliko Dangote, ya ce samun ɗa namiji da ake ganin kamar shi zai ci gaba da riƙe sunan iyalinsa da gadon abin da ya bari ba shi ne babban burinsa ba, duk da yadda al’ummar da ya fito cikinta da ke ba da muhimmanci ga samun ɗa namiji.
Ɗankasuwar mai shekaru 69 ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabajin na ARISE News, lokacin da aka tambaye shi ko har yanzu yana fatan samun ɗa namiji.
Dangote ya ce: “Wannan, a ganina, ba shi ne babban burina ba. Bari in faɗa kai-tsaye. Ba shi ne babban burina ba, domin a yau kamar yadda muke magana, Allah ne ke sarrafa komai.”
Ya bayyana cewa duk da cewa mutane na iya yin addu’ar samun ɗa namiji, samun ɗa ba lallai ne ya tabbatar da cewa sunan iyali da gadonsa za su ci gaba da kasancewa ba.
Ya ce: “Wani lokaci kana iya roƙon Allah Ya ba ka ɗa namiji, amma wannan ɗan shi ne zai iya ɓata sunan zuri’ar da jefa ta cikin matsala. Don haka, wani lokaci idan Allah bai ba ka wani abu ba, ka da ka matsa.”
Dangote, wanda yake da ’ya’ya mata uku, ya ƙara da cewa bai yi imanin samun ɗa namiji zai haifar da sakamako mafi kyau fiye da abin da ’ya’yansa mata ukun suka cimma ba.
Ya ce: “Ban yi imanin cewa da na samu ɗa namiji da zai yi abin da ya fi abin da waɗannan ’ya’ya mata uku nawa suka yi ba.”

















