Sakataren Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya ce za a dakatar da ayyukan dukkan kamfanonin jiragen saman Iran a duniya daga ranar Laraba.
Bessent ya shaida wa gidan talabijin na Amurka CNBC a ranar Litinin cewa, “A ranar 23 ga Satumba, za a dakatar da dukkan kamfanonin jiragen saman Iran a duniya,” yayin da yake bayyana sabbin takunkuman da Amurka ke shirin kakabawa da nufin ware harkokin sufurin jiragen saman farar hula na Iran.
Ya ce filayen jiragen saman kasa da kasa da ke kula da jiragen Iran za su fuskanci cikakken katsewa daga tsarin hada-hadar bankunan Amurka.
Bessent ya yi gargadin cewa kamfanonin kasashen waje ba za su iya samar wa jiragen Iran man fetur, ba su wurin sauka ko sayar da tikitin fasinjoji ba tare da fuskantar barazanar rasa damar amfani da tsarin hada-hadar dalar Amurka ba.
Jami’an Iran ba su fitar da martani a hukumance nan take kan shirin takunkuman da suka shafi harkokin jiragen saman ba.
Wannan matakin na takaita zirga-zirgar jiragen saman Iran na zuwa ne yayin da Washington ke kara tsaurara matakan tattalin arziki kan Tehran karkashin shirin Operation Economic Fury, a daidai lokacin da yakin Iran ya shiga wata na bakwai.
Yakin ya fara ne a karshen watan Fabrairu bayan jerin hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai tare, lamarin da ya haddasa matsaloli a harkokin safarar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, musayar hare-haren makamai masu linzami a yankin, da kuma kara matsin lamba kan hanyoyin kasuwanci da harkokin kudi na Iran.

















