Gwamnatin Burkina Faso ta bayyana cewa an dakile wani yunkuri na kifar da gwamnatin shugaba Ibrahim Traoré, tare da zargin tsohon shugaban kasar Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba da kitsa shirin. Ministan tsaro, Mahamadou Sana, ne ya sanar da hakan a daren Talata ta gidan talabijin na kasar RTB, inda ya ce jami’an leƙen asiri sun gano shirin tun kafin aiwatar da shi, tare da nuna godiya ga ƙwarewar hukumomin tsaro.
Ministan ya bayyana cewa an tsara shirin ne ranar Asabar da ta gabata, inda ake zargin za a kashe manyan jami’an gwamnati na soja da fararen hula, tare da kisan Kyaftin Traoré ta hanyar harbi daga kusa ko kuma sanya bam a gidansa. Ya ce shirin ya haɗa da lalata sansanonin jirage marasa matuƙa (drones) da kuma yiwuwar turo dakarun ƙasa daga ƙasashen waje.
A cewarsa, tsohon shugaban ƙasar Damiba ne ake zargi da jagorantar shirin tare da samar da kuɗi, ɗaukar hayar sojoji da fararen hula, da kuma shirya matakan samun goyon bayan jama’a. Sana ya ce saboda dalilai na tsaro, ba za a fitar da cikakkun bayanai kan wasu sunayen ba tukuna, amma gwamnati za ta saki bidiyoyin da ke nuna mutanen da ake zargi da rawar da suka taka a lamarin.














