Hukumomi a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da wata ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama sun ce an gano manyan ƙaburbura biyu ɗauke da gawarwaki kusan 170 a lardin South Kivu, a yankin da ‘yan tawaye na M23 suka bar kwanan nan. Gwamnan lardin, Jacques Purusi, ya ce an gano kaburburan ne a Kiromoni da Kavimvira, kusa da birnin Uvira.
A cewarsa, an samu kimanin gawarwaki 30 a Kiromoni kusa da iyakar Burundi, yayin da a Kavimvira aka gano gawarwaki 141. Wata ƙungiya mai fafutukar kare fararen hula ta ce ta nemi shiga wuraren don bincike, amma sojojin Kongo sun hana su.
Masu fafutukar sun zargi M23 da kashe mutanen, suna cewa an yi musu zargin kasancewa sojoji ko masu goyon bayan gwamnati. Haka kuma, bangarorin biyu — sojojin Kongo da M23 — sun sha fuskantar zarge-zargen cin zarafin bil’adama.
Gano kaburburan na zuwa ne a lokacin da rikici ke ƙara tsananta a gabashin ƙasar, duk da yunƙurin sulhu da aka yi a baya. Rikicin ya janyo tarwatsewar fararen hula da kuma tsanantar rashin tsaro a yankin.














