Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da soke ayyukan daruruwan ƙungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da na ƙasashen waje, bayan da aka ce sun kasa cika ƙa’idojin da doka ta tanada don ci gaba da aiki a ƙasar.
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Nijar ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan binciken da aka gudanar tsakanin ranakun 14 zuwa 15 ga Nuwamba, inda aka gano cewa ƙungiyoyi da dama ba su gabatar da muhimman takardunsu na ayyuka ba, duk da an sanar da su tun da wuri.
Daga cikin sama da ƙungiyoyi 3,000 da ke aiki a Nijar, ƙungiyoyi 1,684 na cikin gida ne kawai suka cika sharudda, yayin da ƙungiyoyi 125 na ƙasashen waje suka samu amincewa.
A cewar gwamnati, ƙungiyoyi 1,809 ne kacal suka cancanci ci gaba da gudanar da ayyukansu, kuma an wallafa cikakken jerin sunayensu a cikin takardun hukuma na ƙasar.
Ma’aikatar ta jaddada cewa duk ƙungiyar da ba ta cika sharuddan doka ba, ba za a ba ta damar ci gaba da aiki a Nijar ba.














