Ƙasar Belgium na shirin cire iyakar shekarun shiga aikin soja a matsayin reservist domin faɗaɗa ɗaukar ma’aikata da jawo ƙwarewa daga sassa daban-daban. Dan majalisa Peter Buysrogge na jam’iyyar New Flemish Alliance ya gabatar da kudirin doka da zai soke iyakar shekaru 34 ga reservist na yau da kullum, tare da soke iyakar shekaru 50 ga jami’an reservist. A cewarsa, mutane da dama masu sha’awa na rasa damar shiga ne saboda wadannan ka’idoji, lamarin da ke hana rundunar amfani da gwanintarsu.
A Belgium, reservist na aiki ne bisa son rai tare da ayyukan farar hula, inda sojoji ke amfana da ƙwarewa na musamman—daga masana kwamfuta zuwa direbobin manyan motoci—lokacin da ake bukata. Ma’aikatar Tsaro na da burin ɗaukar akalla reservist 1,000 duk shekara, kuma tana fatan cire iyakar shekaru zai taimaka cimma hakan. Matakin na zuwa ne a lokacin da gwamnatin Firayim Minista Bart De Wever ke ƙara kasafin tsaro domin cimma burin NATO na kashe kashi 2% na GDP a fannin tsaro.
Majiyar Labari: AA














