Afirka Duniya Siyasa

Sahel: Burkina Faso, Mali da Nijar sun soki kama Maduro da Amurka ta yi

Ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar sun yi Allah wadai da kama Shugaban Venezuela Nicolas Maduro, suna kiran matakin Amurka keta dokar ƙasa da ƙasa.

Newstimehub

Newstimehub

8 Jan, 2026

6e149a5ed2ce5d747df5d0f644f77b5ddc4dedb939dcd956229fc672dbc2a22e main

Ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar sun yi kakkausar suka ga matakin Amurka na kama Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, suna bayyana shi a matsayin tsoma baki da kuma hari ga ikon wata ƙasa mai cin gashin kanta.

A wata sanarwa da Kungiyar Ƙasashen Sahel ta fitar, an ce ƙasashen ukun sun “yi Allah wadai matuƙa” da abin da ya faru, tare da zargin cewa an karya dokokin ƙasa da ƙasa. Sun kuma buƙaci Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya ɗauki mataki domin dawo da doka da oda a Venezuela.

Sanarwar, wadda Shugaban Burkina Faso Kaptin Ibrahim Traoré ya sanya wa hannu, ta bayyana kama Maduro da Shugaba Donald Trump ya amince da shi a matsayin “tsoma baki da ba za a yarda da shi ba”.

Rahotanni sun ce sojojin Amurka sun kama Maduro da matarsa a Caracas, inda aka kai su New York domin fuskantar shari’a kan zargin miyagun ƙwayoyi da makamai — zarge-zargen da Maduro ya musanta.

Majiyar Labari: TRT HAUSA