Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a Yamai, babban birnin Nijar, ranar Laraba domin nuna goyon bayansu ga shugaban gwamnatin sojin ƙasar, Janar Abdourahamane Tiani, da kuma sojojin ƙasar, bayan dakile wani yunƙurin tawaye a cikin rundunar sojin a ƙarshen mako, kamar yadda kafafen yaɗa labaran cikin gida suka ruwaito.
Zanga-zangar ta zo ne kwanaki kaɗan bayan magoya bayan gwamnatin sojin sun dakile yunƙurin tayar da zaune tsaye.
Dubban ’yan Nijar sun samu halartar zanga-zangar da aka gudanar a Yamai, ciki har da wasu ministocin gwamnati.
Kafafen yaɗa labaran gwamnati sun ce an shirya gudanar da wasu zanga-zangar makamancin haka a manyan biranen ƙasar.
Ministan Kasuwanci, Abdoulaye Seydou ya ce zanga-zangar za ta nuna wa duniya cewa “al’ummar Nijar suna da haɗin kai”, kuma “cin amana ba zai karya ƙudurinmu ba.”
Shugaban ma’aikatan Janar Tiani, Janar Amadou Ibro ya kuma zargi wasu ƙasashen waje da hannu wajen yunƙurin tawayen, yana mai cewa “masu ɗaukar nauyinsa suna ƙasashen waje.”
A baya, gidan talabijin na ƙasar ya zargi Faransa, tsohuwar ƙasar da ta yi wa Nijar mulkin mallaka, da hannu a yunƙurin tawayen.
Kamar maƙwabtan Nijar da ke karkashin mulkin soji, wato Burkina Faso da Mali, Nijar ta kuma ƙara nisanta kanta da Faransa.

















