Afirka

Dubban Mutane Sun Halarci Jana’izar Saif al-Islam Gaddafi a Libya

Dubban Mutane Sun Halarci Jana’izar Saif al-Islam Gaddafi a Arewa maso Yammacin Libya

Newstimehub

Newstimehub

6 Feb, 2026

1770389204068 4tqkr c4c37caa9cbc25b22f50a07b8bff8205256d52d438b913f4b13df0b3b75fb87f

Dubban mutane sun taru a ranar Juma’a a arewa maso yammacin Libya domin jana’izar Saif al-Islam Gaddafi, ɗa kuma magajin marigayi tsohon shugaban ƙasar Libya, Muammar Gaddafi, wanda aka kashe a farkon wannan makon bayan wasu mahara huɗu sun kutsa gidansa suka harbe shi.

An gudanar da jana’izar a garin Bani Walid, mai nisan kilomita 146 kudu maso gabashin Tripoli, inda masu makoki suka ɗauki akwatin gawarsa tare da ɗaga hotunansa da na mahaifinsa.

A cewar hukumomin Libya, an kashe Saif al-Islam mai shekaru 53 a ranar Talata a gidansa da ke Zintan, mai nisan kilomita 136 kudu maso yammacin Tripoli. Binciken farko ya nuna cewa an harbe shi har lahira, yayin da ƙungiyarsa ta siyasa ta ce mutanen da suka aikata kisan sun kasance huɗu sanye da abin rufe fuska, waɗanda suka kashe kyamarorin tsaro kafin su aiwatar da abin da suka kira “kisan gilla mai tsanani da yaudara.”

Saif al-Islam shi ne ɗaya daga cikin fitattun ’ya’yan Muammar Gaddafi, wanda ya mulki Libya tsawon fiye da shekaru 40 kafin a hambarar da shi a 2011 kuma daga bisani aka kashe shi a Sirte. Masu sharhi na ganin cewa kisan Saif al-Islam na iya ƙara ta’azzara rikicin siyasa da na tsaro a Libya, ƙasar da har yanzu ke fama da rarrabuwar kai da rikice-rikice tun bayan faɗuwar gwamnatin Gaddafi.

Majiyar Labari: TRT HAUSA