Yarima Mohammed bin Salman na Saudiyya ya samu tarba mai kyau daga Trump a Fadar White House

Shugabannin biyu za su bayyana yarjejeniyar biliyoyin daloli, ciki har da ta sayar wa jiragen yakin F-35 na Riyadh, sannan su yi zama da mataimakansu don tattauna hanyoyin warware matsalolin Gabas ta Tsakiya kafin wani taron manema labarai.
19 Nov, 2025
Trump ya sayi takardun lamuni na aƙalla dala miliyan 82 tun daga Agustan 2025 – Bayanai

Bayanai sun nuna cewa Trump ya sayi takardun lamuni a kamfanonin da suke amfana da munfofi da tsare-tsaren gwamnatinsa waɗanda suka haɗa da kamfanin Meta, Qualcomm da JP Morgan da wasu jerin kamfanoni.
17 Nov, 2025
Koriya ta Kudu ta nemi yin tattaunawar soji da Koriya ta Arewa don kaucewa rikicin kan iyaka

Seoul ta yi kira da ayi tattaunawar soji ta Korea da nufin rage zaman ɗar-ɗar da kuma fayyace layin kwance ɗamara, bayan sojojin Korea ta Arewa sun ringa tsallake iyaka ba sau ɗaya ba sau biyu ba.
17 Nov, 2025
Trump ya bayar da umarnin haramta wa masu ƙiba shiga Amurka

Wannan shi ne sabon matakin da Shugaba Donald Trump ya ɗauka don ƙin yarda da baƙin-haure a matsayin wani ɓangare na matakansa na taƙaita shige da fice.
15 Nov, 2025

COP30: Manyan masu gurbata muhalli na duniya ba su je taron sauyin yanayi na Brazil ba

Rasha ta ce tana sa ido kan Nijeriya bayan barazanar da Trump ya yi ta kai hari kasar

Zohran Mamdani: Matashi Musulmi na farko ya lashe zaɓen Magajin Birnin New York

Rundunar Sojin Ruwan Pakistan ta kama mugwayen ƙwayoyi na dala biliyan ɗaya a Tekun Arebiya

Putin ya gargaɗi Trump cewa bai wa Ukraine makamai mai linzamin Tomahawk zai jawo matsala tsakaninsu
17 Oct, 2025
Yadda hukumomi a India suke farautar Musulmai da suke cewa ‘Ina son Annabi Muhammad’
A faɗin jihohin da jam’iyyar BJP ke mulki, bayyana ra’ayin addini na iya janyowa a kama mutum da kuma rushe masa gida, abin da yake haifar da damuwa sosai kan damar Musulmai ta ‘yancin addini da bayyana kan su a Indiya.

4 Oct, 2025
An naɗa Sarah Mullally mace ta farko Shugabar Cocin Ingila
Sarki Charles III ya amince da naɗin Mullally bayan Justin Welby ya yi murabus sakamakon wani rahoto ya gano Cocin Ingila ta yi rufa-rufa kan cin zarafin yara maza a shekarun 1970s, kuma bai sanar da hukumomi ba a lokacin da aka sanar da shi a 2013.

30 Sep, 2025
An tsinci gawar jakadan Afirka ta Kudu a Faransa a wajen otal a birnin Paris
Rahotanni na cewa jami’in na diflomasiyya mai shekara 58 ya diro ne daga hawa na 22 a hotel ɗin a Paris, amma an ƙaddamar da bincike, a cewar masu shigar da ƙara.

30 Sep, 2025
Babban Alkalin Kotun Amurka ya dakatar da umarnin Trump na korar ma’aikatan VOA
Babban Alkalin kotun tarayya ya dakatar da shirin gwamnatin Trump na korar ma’aikatan Muryar Amurka sama da 500, yana mai zargin shugabannin hukumar da suka hada da Kari Lake da kin bin umarnin kotu kan tabbatar da dokokin aikin jarida na VOA.

26 Sep, 2025
An yanke wa tsohon Shugaban Faransa Sarkozy hukuncin shekara biyar a gidan yari
Kotun ta umarci cewa a tsare Sarkozy zuwa wani lokaci, tare da bai wa masu gabatar da kara wata daya su sanar da tsohon shugaban kasar lokacin da zai fara zaman gidan yari.

24 Sep, 2025
UNGA 80: Trump ya yi alkawarin hana Isra’ila shirin ƙwace Yammacin Kogin Jordan
Shugabannin Ƙasashen Musulmai sun matsa wa Trump lamba kan ya yi gaggawar goyon bayan samar da tsagaita wuta a Gaza, da shigar da tallafi da samar da tsarin ‘yancin kan Falasɗinu, suna gargadin samun tashin hankali a yankin in aka ci gaba da yaƙin.

24 Sep, 2025
Amazon da Microsoft sun buƙaci ma’aikatansu su zauna a Amurka bayan bizar H-1B ta koma $100,000
Bayan dokar da Trump ya saka wa hannu, duk wani kamfanin Amurka da ke so ya ɗauko ma’aikaci daga ƙasar waje, sai ya rinƙa biya wa ma’aikacin dala 100,000 a duk shekara a matsayin kuɗin biza.

18 Sep, 2025
Yankin Kerala na India na fama da wata cuta da ke cinye ƙwaƙwalwa
Ana kamuwa da cutar ‘Naegleria fowleri’ da ba a saba gani ba a wuraren ninkaya marasa tsafta, wuraren wasan ruwa da sauran wuraren nishadi.

11 Sep, 2025
Trump ya yi tattaunawa mai zafi da Netanyahu kan harin Isra’ila a Qatar – Rahotanni
Rahotanni sun ce Netanyahu ya shaida wa Trump cewa ya samu wata ‘yar ƙaramar dama ce ta kai wa Qatar hari inda ya yi amfani da damar.

11 Sep, 2025
Austria za ta haramta wa ɗalibai ‘yan ƙasa da shekaru 14 sa ɗankwali da hijabi
Duk wanda bai bi umarnin ba za a gana da iyayensa, kuma za a ci su tara daga $175 zuwa $1,170.


