Rahotanni sun nuna cewa a kudancin birnin Lyon, manoman Faransa sun ci gaba da zanga-zangar rufe hanyoyi tun daga Litinin, inda suka kafa shinge da manyan taraktoci a kan manyan hanyoyi.
Hanyar M7 an rufe ta gaba ɗaya a yankin Pierre-Bénite, inda masu zanga-zangar suka kafa sansani, alamar cewa matakin na iya ɗaukar kwanaki idan ba a cimma matsaya da hukumomi ba. Haka kuma an samu cunkoso da rufe wasu sassan hanyar haɗin A450/A7, lamarin da ya tilasta hukumomin hanya su kafa sabbin hanyoyin karkata da gargadin direbobi su guji yankin.
Manoman na nuna adawa ne da wasu manufofin gwamnati, ciki har da yadda ake tafiyar da cutar dabbobi (Lumpy Skin Disease), hauhawar farashin kayan samarwa, da kuma yarjejeniyar kasuwancin EU-Mercosur wacce ke baiwa kayayyakin gonar kasashen Kudancin Amurka damar shiga kasuwar Turai cikin sauki.
A cewar bayanai, yarjejeniyar na baiwa kayayyakin naman sa, kaji, madara, sukari da ethanol daga ƙasashen Brazil, Argentina, Paraguay, Uruguay da Bolivia damar samun rangwamen haraji, abin da manoman Turai ke ganin zai kara musu matsin lamba.














