Duniya

FIFA ta sauƙe lafari ɗan Somaliya Artan daga Gasar Kofin Duniya bayan Amurka ta hana shi shiga ƙasar

Hukumar FIFA ta ce ba ta da ƙarfin iya sauya matakin da aka ɗauka kan shigar Omar Artan ƙasar, inda ta ce saboda Amurka ce mai masaukin baƙi tana da hurumin bayarwa ko hana bizar shiga ƙasarta.

Newstimehub

Newstimehub

9 Jun, 2026

5b1a000f0777b85ab3d79a96dc66b8f6c6627bfc8feb21a1dca9557ba30b1e36

An cire sunan lafarin Somaliya mai lambar yabo Omar Artan daga cikin waɗanda za su hura wasanni a gasar cin kofin duniya bayan an hana shi shiga Amurka, kamar yadda hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ta bayyana ranar Litinin.

Wani mai magana da yawun FIFA ya tabbatar a wata sanarwa cewa Artan, wanda aka hana shiga Amurka bayan ya isa filin jiragen sama na Miami a ranar Asabar, ba zai taka wata rawa ba a gasar cin kofin duniya.

Da ba don haka ba da Artan zai zama lafarin Somaliya na farko da zai hura wasa a gasar cin kofin duniya .

“FIFA ta tabbatar da cewa jami’in wasa Omar Abdulkadir Artan ba zai iya atisaye da kuma alƙalanci a gasar cin kofin duniya ta hukumar FIFA ta shekarar 2026 ba bayan an hana shi shiga Amurka,” kamar yadda mai magana da yawun hukumar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.

FIFA ba ta iko

FIFA ta jaddada cewa ba ta da ƙarfi wajen iya sauya matakin da aka ɗauka, wanda ta ce alhaƙin ɗaya daga cikin ƙasashe masu masauƙin baƙi (Amurka) ne.

“FIFA ba ta da hannu a yanayin bayar da biza na ƙasar mai masauƙin baƙi, ciki har da hukunce-hukunce na biza kuma hukumomi sun sanar da ita cewa ba za a sauya matsayi -[kan] Mista Artan ba a halin yanzu,” a cewar mai magana da yawun hukumar.

“Bisa gasannin FIFA na baya, gwamnatin ƙasa mai masauƙin baƙi ce kawai ke da alhaƙin tabbatar da wanda zai samu biza da kuma wanda za a bai wa damar shiga ƙasar.”

Wani mai magana da yawun hukumar da ke hana fasa ƙwauri da kare kan iyakar Amurka (CBP) ya ce an hana Artan shiga ƙasar ne bayan an yi bincike na yau da kullum.

“A yayin tantancewa, an sake ƙarin bincike kan matafiyin, wani ɓangare na yau da kullum na binciken CBP a lokacin da jami’ai ke buƙatar tantance ko wane bayani ko kuma tabbatar da yiwuwar ba da damar shiga ,” in ji mai magana da yawun CBP.

“Bayan binciken, matafiyin wanda wani lafiri ne na gasar cin kofin duniya na FIFA, an tabbatar da cewa bai kamata a ba shi damar shiga ba sakamkon damuwa na bincike kuma an hana shi shiga .”

Haramta tafiyar Trump

Somaliya, ɗaya ce daga cikin ƙasashen da sunayensu ke cikin jerin sunayen ƙasashen da gwamnatin Shugaba Donald Trump ta hana shiga ƙasar a wani ɓangare na yaƙi da kwarar baƙi zuwa ƙasar.

A wata sanarwar da ya tura wa kamfanin dillancin labaran AFP, Artan ya ce yana son ya mayar da hankali kan makomarsa.

“Duk da yanayin, ina cikin hayyacina sosai kuma na mayar da hankali kan ƙalubale na gaba a aiki na alƙalancin wasa,” in ji shi.

“Ina so na gode wa abokanan hulɗa na ƙwallon ƙafa domin saƙonninsu kuma na yi wa abokan aikina fatan nasara a gasar cin kofin duniya kuma ina fatan na sake haɗuwa da su a gasanni na gaba .”

Halastacciyar biza

Wani mai bai wa gwamnati shawara a Mogadishu ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP daga farkon ranar Litinin cewa Artan yana da halastacciyar biza ta shiga Amurka .

Za a fara gasar ne ranar Alhamis.

“Omar Artan yana cikin lafarin da aka fi girmamawa a Afrika kuma ya cancanci goyon bayan dukkan masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa,” a cewar Ciise Aden Abshir, wani babban mai ba da shawara ga ma’aikatar matasa da wasanni ta Somaliya kuma tsohon keftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar.

Abshir ya ce Artan ya bi jirgi ya koma Istanbul bayan an hana shi shiga a Miami.

“Hana shi shiga Amurka da kuma hana shi alƙalancin wasannin da aka shirya ba shi kawai ne ya yi wa lahani ba amma ya yi zagon ƙasa ga jajircewar ƙwallon ƙafa wajen tabbatar da adalci da cancanta da kuma tunanin adalci,” kamar yadda Abshir ya bayyana .

Artan yana cikin lafari 52 da hukumar FIFA ta sanar da sunayensu a matsayin waɗanda za su hura wasannin gasar cin kofin duniya a Kanada da Mexico da kuma Amurka .

Lafari na shekara

Ya kasance yana alƙalancin wasanni a gasar lig ɗin ƙwallon ƙafar ƙasar Somaliya tun da ya zama lafarin hukumar FIFA a shekarar 2018, kuma ya hura wasa a gasar cin kofin Afirka ta baya-bayan nan.

A shekarar 2025 hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka ta bayyana sunansa a matsayin lafarin da ya fi fice a ƙwallon ƙafa na maza a shekarar.

Shugaban ƙasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya yaba wa Artan a watan Afrilu bayan ya kafa tarihi a matsayin ɗan Somaliya na farko da aka fara zaɓa domin hura wasa a gasar cin kofin duniya .

“Na yaba wa ƙoƙari da ƙwarewa da kuma gaskiya da riƙon amana da lafari Omar ya nuna , inda ya zama wata alama ta ƙarfin gwiwa ga ‘yan Somaliya masu tasowa,” in ji Mohamud.