Erling Haaland ya shiga cikin jerin ‘yan wasa 35 da suka kafa tarihin cin ƙwallo 100 a Premier League, bayan da Manchester City ta doke Fulham da ci 5-4, kuma shi ne ya fara zura ƙwallon farko a wasan da aka buga a Craven Cottage. Tauraron Norway ɗin ya cimma wannan bajinta cikin wasanni 111 kacal, abin da ya sa ya zarce Alan Shearer wanda ya kai matsayi iri ɗaya a shekarar 1995 bayan wasanni 13 fiye da shi.
Yanzu haka, Haaland na kan ƙalubalantar tarihin Shearer na samun ƙwallaye 260 mafi yawa a tarihin Premier League. Haaland ya kuma tsawaita zamansa a Etihad Stadium har zuwa kakar 2033/34, domin ci gaba da taka leda tare da Manchester City.













