Rahotanni sun nuna cewa sama da makamai masu linzami da harsasai masu jagora guda 3,000 aka yi amfani da su a cikin sa’o’i 36 na farko na hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran. Wannan mataki ya nuna irin girman hare-haren da kuma damuwar da ake yi kan yadda za a samar da wadannan makamai idan rikicin ya ci gaba.
Binciken Payne Institute ya nuna cewa Iran ma ta mayar da martani da makamai sama da 1,000 a yankin, ciki har da kimanin 380 ballistic missiles, 700 Shahed drones, da kuma wasu makaman kariya ta sama. Wannan ya sa Amurka, Isra’ila da wasu kasashen yankin Gulf suka yi kokarin dakile wadannan hare-hare ta hanyar tsarin kariya na iska.
A bangaren hare-haren farko, sojojin Amurka sun yi amfani da makamai daban-daban da suka hada da JDAM bombs, Tomahawk cruise missiles, drones masu rahusa, da kuma makaman AGM-88 domin lalata tsarin radar na Iran. A lokaci guda, Isra’ila ma ta kai hare-hare masu yawa ta amfani da makamai kamar Spice guided bombs, Rampage missiles, da kuma makaman Delilah.
Haka kuma an yi amfani da manyan tsarin kariya domin dakile hare-haren Iran, ciki har da Patriot, THAAD, Iron Dome, da Arrow. Sai dai masana sun ce yawan makaman da aka kashe da tsadar su na iya zama babban kalubale ga samar da su nan gaba, musamman saboda wasu muhimman kayan da ake amfani da su kamar cobalt, tungsten da rare earths suna fitowa daga kasashe kalilan, ciki har da China.














