Hukumar Kula da Sadarwa (HAC) ta Jamhuriyar Gabon ta sanar da dakatar da amfani da shafukan sada zumunta a fadin kasar baki daya, har sai an sake bayar da sanarwa. Matakin, wanda aka bayyana a ranar Talata, ya biyo bayan damuwa kan abubuwan da ake yadawa a dandamalin intanet.
A cikin sanarwar da aka karanta a gidan talabijin na kasa Gabon 1ère, kakakin HAC Jean-Claude Mendome ya ce an dauki matakin ne domin dakile yaduwar sakonnin da aka bayyana a matsayin marasa dacewa, na batanci, na tsana da kuma cin zarafi. Hukumar ta ce irin wadannan abubuwa na cutar da mutunci, hadin kan jama’a, tsaron kasa da kwanciyar hankalin cibiyoyin gwamnati.
HAC ta kuma nuna damuwa kan yawaitar labaran karya, cin zarafin yanar gizo da kuma fallasa bayanan sirri ba tare da izini ba. A cewar hukumar, wadannan matsaloli na iya haddasa rikice-rikicen zamantakewa tare da barazana ga hadin kan kasa.
Hukumar ta jaddada cewa ‘yancin fadin albarkacin baki hakki ne na asali, amma dole ne a yi amfani da shi cikin bin dokokin kasa da na kasa da kasa. Ba a bayyana takamaiman shafukan da matakin ya shafa ko tsawon lokacin dakatarwar ba.
Majiyar Labari: AA














