Hukumomin Rwanda sun yanke shawarar rufe sama da majami’u 10,000 na cocin Kiristocin Bishara (Evangelical) bayan da aka gano cewa ba su cika sharuddan dokar da aka kafa tun 2018 ba, wadda ke tsara yadda ake gudanar da wuraren ibada a ƙasar. Dokar ta ƙunshi tsauraran ƙa’idoji da suka shafi lafiyar jama’a, tsaro, gaskiya a harkokin kuɗi, tare da buƙatar duk masu wa’azi su samu horo na musamman kafin su fara aikin wa’azi.
Shugaba Paul Kagame ya sha sukar yawaitar majami’un bishara a Rwanda, yana zargin wasu daga cikinsu da rashin bayar da gudummawa ga ci gaban al’umma, tare da alaƙanta wasu da sata ko ɓoye ‘yan daba.
Duk da cewa mafi yawan ‘yan ƙasar Kiristoci ne, rufe dubban majami’u ya tilasta wa mutane da dama yin tafiya mai nisa domin yin ibada, bisa dokar 2018 da ta tanadi tsauraran ƙa’idoji. Wasu malaman coci sun ce dokar ta fi shafar sabbin majami’u, yayin da wasu masana ke danganta matakin da tarihin kisan ƙare-dangi na 1994 da kuma matsalolin tsaro, duk da amincewa da rawar da addini ya taka wajen warkar da raunukan tunani a ƙasar.














