Rikicin da ke ƙara ƙamari a yankin ya sake ɗaukar sabon salo bayan babban hafsan sojin Isra’ila, Eyal Zamir, ya sanar da fara wani farmaki mai tsanani kan Lebanon wanda zai ɗauki kwanaki da dama. Matakin na zuwa ne bayan ƙungiyar Hezbollah ta ce ta harba makamai masu linzami zuwa Isra’ila cikin dare, tana mai cewa ta nufi kudancin birnin Haifa.
Zamir ya bayyana cewa hare-haren za su mayar da hankali ne kan wuraren da Hezbollah ke amfani da su, yana mai cewa dole ne a shirya wa wani dogon rikici. Ya ƙara da cewa sojojin Isra’ila za su ci gaba da kai hare-hare a jere, mataki bayan mataki, har sai an cimma manufarsu. Tun da farko, kwamandan yankin arewa na sojin Isra’ila, Birgediya Janar Rafi Milo, ya riga ya sanar da ƙara zafafa farmaki kan Lebanon.
Bayan mutuwar Jagoran Addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei a harin haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila, Hezbollah ta shiga sahun ramuwar gayya ta hanyar harba makamai da rokoki zuwa Isra’ila. A martanin haka, sojojin Isra’ila sun ƙaddamar da hare-haren sama a sassa daban-daban na Lebanon.














