Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar beli da tsohon Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami, ya gabatar zuwa ranar 7 ga Janairu, yayin da yake tsare a gidan gyaran hali na Kuje bisa zargin safarar kuɗi.
Malami, tare da ɗansa Abdulaziz da ɗaya daga cikin matansa, na fuskantar tuhume-tuhume guda 16 da EFCC ta shigar, inda ake zarginsu da wanke kuɗaɗen haram da darajarsu ta kai naira biliyan 8.7. Dukkaninsu sun musanta laifin da ake tuhumarsu da shi lokacin gurfanar da su a ranar 29 ga Disamba, 2025.
EFCC ta ce laifukan sun faru ne tsakanin 2015 da 2025, inda ake zargin an yi amfani da kamfanoni, asusun bankuna da kuma sayen kadarori masu tsada a Abuja da wasu jihohi domin ɓoye asalin kuɗaɗen. Kotun ta bayar da umarnin tsare su a Kuje har zuwa lokacin yanke hukunci kan belin.














