Duniya

Ladanin Masallacin Annabi a Madina, Sheikh Faisal Nouman, Ya Rasu

Sheikh Faisal Nouman, ladanin Masallacin Annabi a Madina tun 2002, ya rasu bayan fama da jinya.

Newstimehub

Newstimehub

25 Dec, 2025

download 2 1

Ladanin Masallacin Annabi (SAW) da ke birnin Madina, Sheikh Faisal Nouman, ya rasu bayan shafe wani lokaci yana fama da jinya, kamar yadda hukumomi a Saudiyya suka sanar.

Sheikh Faisal ya rasu ne a ranar Laraba a Madina. An naɗa shi a matsayin ladanin masallacin a shekarar 2002, inda ya gaji kakansa da mahaifinsa a wannan muƙami mai daraja, wanda ya dade yana riƙewa a cikin iyalinsu.

Majiyar Labari: BBC Hausa