Cikin alhini da jimami, Libya ta ayyana zaman makoki na ƙasa bayan wani hatsarin jirgin sama a Turkiyya da ya yi sanadiyyar rasuwar Babban Hafsan Sojojin ƙasar, Mohammed al-Haddad, tare da wasu manyan jami’an soji.
Gwamnatin Haɗin Kan Ƙasa ta Libya ta sanar a ranar Talata cewa za a yi zaman makoki na kwanaki uku, inda za a sauke tutoci rabin sanda a dukkan cibiyoyin gwamnati, tare da dakatar da duk wasu taruka da bukukuwa na gwamnati.
A cikin sanarwar, gwamnati ta miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan da abokan aikinsu a Rundunar Sojin Libya, tana mai addu’ar Allah ya ji ƙansu kuma ya ba iyalansu haƙuri.
Shugaban Majalisar Shugabancin Libya, Mohamed Menfi, ya bayyana mutuwar a matsayin “babban rashi ga rundunar soji da al’ummar ƙasa,” yana mai yabawa mamatan bisa sadaukarwa, jajircewa da biyayya wajen hidimar ƙasa.
A nasa ɓangaren, Ministan Cikin Gida na Turkiyya, Ali Yerlikaya, ya ce an gano ɓaraguzan jirgin haya samfurin Falcon 50 a kudancin Haymana, kusa da Ankara, inda jami’an Turkiyya suka tabbatar da mutuwar Babban Hafsan Sojojin Libya da wasu jami’ai hudu.














