Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya nuna matukar damuwa kan yadda rikicin Gabas ta Tsakiya ke kara tsananta, musamman bayan sabbin hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran.
Kakakin majalisar, Stephane Dujarric, ya bayyana cewa sakataren yana bibiyar halin da ake ciki cikin tsananin damuwa saboda ana ganin rikicin yana kara bude sabbin bangarori na fada a yankin.
A cewarsa, rikicin ya riga ya jawo karuwar mace-macen fararen hula da kuma matsanancin tasirin jin kai ga al’ummomi a yankin. Haka kuma ya gargadi cewa hare-haren da ake kai wa kayayyakin makamashi a yankin Tekun Fasha na iya girgiza tattalin arzikin duniya, ganin yadda kasashe da dama har yanzu ke dogaro sosai da makamashin mai da gas.
Dujarric ya kara da cewa ayyukan agaji na jin kai suna fuskantar manyan matsaloli saboda rashin tsaro, katsewar hanyoyin samar da kayayyaki da kuma rufe sararin samaniya. Ya jaddada cewa dole ne a mutunta dokokin jin kai na kasa da kasa, tare da kare fararen hula da ma’aikatan agaji.
Haka kuma ya yi Allah wadai da rahotannin wani hari da ya afkawa wata makaranta a kudancin Iran, wanda aka ce ya yi sanadin mutuwar sama da yara mata 160. Ya ce babu kalmomin da za su iya bayyana tsananin wannan mummunan lamari, yana mai kira da a dauki matakin tabbatar da adalci ga wadanda suka mutu.














