A yayin da idon duniya ke kan Moroko saboda ɗaukar nauyin Gasar Ƙasashen Afirka ta AFCON 2025, ƙasar ta ɗauki wani mataki na tarihi ta hanyar fitar da takardun kuɗi da sulalla na musamman, domin tunawa da wannan babbar gasa ta ƙwallon ƙafa da ke gudana a halin yanzu a faɗin ƙasar.
Moroko ta fitar da takardar kuɗi da sulalla don murnar bikin Gasar Ƙasashen Afirka ta AFCON 2025, domin tunawa da kasancewar ƙasar mai masaukin wannan gasa. Babban bankin ƙasar, Bank Al-Maghrib (BAM), ya bayyana cewa kuɗaɗen sun ƙunshi alamomin ƙasa, isharorin ƙwallon ƙafa, da kuma sabbin cibiyoyin wasanni da aka samar a ƙasar.

A cikin wata sanarwa, bankin ya ce ya saki sulen azurfa mai daraja a fuska ta dirhami 250 (kimanin dalar Amurka $27.5), tare da takardar kuɗi mai darajar dirhami 100. Bankin ya jaddada cewa dukkan matakan zayyana da ƙera kuɗaɗen, ƙwararru ‘yan Moroko ne suka aiwatar da su.
Sulallan tunawa da gasar an yi su ne da azurfa da haɗaɗɗen tagulla, kuma suna da nauyin kusan giram 30. A fuskarsu akwai hoton Sarki Mohammed VI, tare da rubuce-rubucen “Mohammed VI” da “Royaume du Maroc” cikin harshen Larabci. An kuma nuna shekarar fitarwa da lambar 1447-2025, wadda aka rubuta da haruffan Larabci da na Tifinagh.
Bankin BAM ya ce takardun kuɗin dirhami 100 suna nuna yadda Daular Moroko ke bai wa wasanni muhimmanci, tare da haskaka sabbin kayayyakin wasanni da aka gina domin karɓar bakuncin gasar. An fitar da kuɗaɗen ne a taƙaitaccen adadi a ranar Litinin, kuma za su yi yawo tare da takardun dirhami 100 na yau da kullum.
A gaban takardar kuɗin akwai hoton Sarki Mohammed VI, tambarin ƙasa, hoton Cibiyar Wasanni ta Yarima Moulay Abdellah da ke Rabat, taswirar Afirka, zanen Moroko da kuma ƙwallon ƙafa.
Moroko na ɗaukar nauyin gasar AFCON karo na 35, wadda aka fara a ranar Lahadi 21 ga Disamba, inda ake gudanar da wasanni a birane da dama a faɗin ƙasar.














