Ƙungiyar National Association of Resident Doctors (NARD) ta sanar da dakatar da yajin aikin ƙasa baki ɗaya da ta shirya, bayan da ta ce an samu ci gaba mai ma’ana a tattaunawa da Gwamnatin Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki.
An cimma matsayar ne a taron gaggawa na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (E-NEC) da aka gudanar ta yanar gizo a ranar 11 ga Janairu, 2026, inda aka duba buƙatun ƙungiyar da sabbin matakan da aka ɗauka. NARD ta ce an kai ga wannan matsaya ne bayan tsoma bakin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sakataren ƙungiyar, Dr Shuaibu Ibrahim, ya bayyana cewa dakatarwar ta wucin-gadi ce kuma da sharadi, domin a sake tantance ainihin abin da aka cimma a taron NEC na gaba da zai fara 25 ga Janairu, 2026.
Rahotanni sun nuna cewa an samu ci gaba a manyan matakai, ciki har da umarni kan biyan bashin albashi da alawus, warware rikicin Asibitin Koyarwa na Tarayya, Lokoja, da kuma aika jerin sunaye kan bashin CONMESS kashi 25% da 35% zuwa IPPIS da Ma’aikatar Kuɗi. Haka kuma, an kafa sabbin kwamitoci domin kula da lokutan aiki, alawus na ƙwarewa, da jin daɗin likitocin horaswa.
NARD ta ce bisa tabbatattun alkawurra daga manyan hukumomi, ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin TICS 2.0 domin bai wa tattaunawar damar samar da sakamako.














