Najeriya

NIN Za Ta Zama Lambar Biyan Haraji (TIN) Daga Janairu 2026 – FIRS

FIRS ta sanar da cewa daga Janairu 2026, lambar NIN za ta zama TIN ga ‘yan Najeriya domin sauƙaƙa biyan haraji da rage kauce masa.

Newstimehub

Newstimehub

23 Dec, 2025

download e1766516693756

A wani mataki da zai sauya yadda ake tantance masu biyan haraji a Najeriya, Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta sanar da cewa daga watan Janairun 2026, lambar zama ɗan ƙasa wato NIN za ta zama lambar biyan haraji (TIN) ga ‘yan Najeriya. Wannan sauyi na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na sauƙaƙa tsarin haraji da kuma rufe gibin da ake amfani da shi wajen kauce wa biyan haraji.

Rahoton da Channels Television ya wallafa ya nuna cewa FIRS ta bayyana hakan ne a wani saƙon wayar da kan al’umma da ta wallafa a shafinta na X. A cewar hukumar, duk ‘yan Najeriya da Hukumar Rijistar Katin Ɗan Ƙasa (NIMC) ta bai wa NIN, wannan lamba ce za ta zama TIN ɗinsu daga shekarar 2026.

Alƙaluman NIMC sun nuna cewa zuwa watan Oktoban 2025, ‘yan Najeriya miliyan 123 da dubu ɗari tara ne suka riga suka samu lambar NIN, lamarin da ke nuna cewa mafi yawan al’umma za su shiga sabon tsarin kai tsaye.

Hukumar FIRS ta kuma bayyana cewa ga kamfanoni, lambobin rijistar da hukumar gwamnati ke bai wa kamfanoni za su kasance lambobin biyan haraji (TIN) a ƙarƙashin sabuwar dokar harajin.

A cewar FIRS, wannan sabon tsari zai taimaka wajen sauƙaƙa gano mutane da kamfanoni, rage matsalar maimaita sunaye, rufe hanyoyin da ake bi wajen guje wa biyan haraji, da kuma tabbatar da cewa duk wanda ke samun kuɗin shiga yana biyan harajin da ya dace da shi.

Sai dai hukumar ta jaddada cewa mutanen da ba su da hanyar samun kuɗin shiga, kamar ɗalibai, ba sa buƙatar lambar biyan haraji a ƙarƙashin wannan tsari.

Majiyar Labari: BBC Hausa