Hukumar Kula da Hidimar Ƙasa (NYSC) ta sanar da cewa sansanin horaswa na Batch A Stream One na shekarar 2026 zai fara aiki a hukumance ranar Laraba, 21 ga Janairu, 2026 a dukkan sansanoni 37 da ke faɗin Najeriya.
A cewar sanarwar, rajistar shiga sansani ga dukkan mambobin hidimar ƙasa (Corps Members) za ta gudana daga ranar 21 ga Janairu zuwa ƙarfe goma sha biyu na dare ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026. Haka kuma, za a gudanar da rantsar da mambobin hidimar ƙasa a ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026.
NYSC ta bayyana cewa bikin rufe sansanin horaswa zai gudana ranar Talata, 10 ga Fabrairu, 2026, bayan kammala cikakken shirin horaswa. Daraktan Janar na hukumar, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ya yi wa dukkan Prospective Corps Members fatan tafiya lafiya zuwa jihohin da aka tura su.
Ya kuma yi gargaɗi ga masu hidimar ƙasa da su guji yin tafiya da dare, tare da bin ka’idojin tsaro yayin tafiya zuwa wuraren sansaninsu domin kare lafiyarsu.














