Hukumar National Youth Service Corps (NYSC) ta sanar da cewa za ta fara amfani da tsari guda da aka daidaita wajen kula da ‘yan hidimar ƙasa masu naƙasa, tun daga lokacin horon Orientation Course har zuwa ƙarshen shekarar hidimarsu.
A cikin wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta NYSC, Caroline Embu, ta sanya wa hannu, Darakta-Janar na hukumar, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ya bayyana hakan a taron bita na gabanin fara horon Batch ‘A’ na shekarar 2026, wanda aka gudanar a Jos, jihar Plateau.
Janar Nafiu ya ce wannan shiri na daga cikin dabarun inganta jin daɗin ‘yan hidimar ƙasa, inda za a fi mayar da hankali ba wai kan bin ƙa’ida kaɗai ba, har ma da mutunci, haɗin kai da bai wa kowa dama iri ɗaya. Ya jaddada cewa NYSC na ƙoƙarin tabbatar da cewa babu wanda aka bari a baya, tare da kafa hukuma mai tausayi da dacewa da bukatun zamani.
Ya kuma yi nuni da muhimmancin amfani da basirar fahimtar motsin zuciya da nuna tausayawa a duk hulɗa da ‘yan hidimar ƙasa da jami’an sansani. A cewarsa, horon Orientation Course shi ne ginshiƙin samun nasarar shekarar hidima, don haka dole ne ya dace da yanayin ƙasa, ƙa’idojin duniya da halayen matasa na zamani.
Daraktan ya ce taron bitar gabanin horon yana da muhimmanci domin tantance ƙalubalen da ke tasowa da kuma samar da sabbin hanyoyi da za su inganta kwarewar hidimar ƙasa, tare da bai wa ‘yan hidima damar shiga al’ummomin da aka tura su cikin sauƙi da kuma zama masu amfani bayan kammala hidima.
Ya yaba wa jami’an NYSC da hukumomin da ke aiki tare da su kan haɗin kai da ya haifar da nasarori a horo na baya, tare da buƙatar mahalarta taron su fito da sabbin dabaru da za su inganta gudanar da sansani, amfani da fasaha da kuma hulɗa da masu ruwa da tsaki.
A nasa jawabin maraba, Daraktan Tsare-tsare, Bincike da Kididdiga, Nura Umar, ya ce taken taron ya nuna muhimmancin horon Orientation Course wajen gina ɗabi’a, kishin ƙasa da halayen ‘yan hidimar ƙasa. Ya ƙara da cewa horon zai ci gaba da dasa ladabi da muhimman ƙa’idojin NYSC a zukatan masu yi waƙilin ƙasa.














