Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta fito fili ta ce babu wata hanya da za ta kawo ƙarshen rikicin siyasar jihar face tsige Gwamna Siminalayi Fubara daga muƙaminsa.
‘Yan majalisar sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da suka gudanar a Port Harcourt, inda suka tabbatar da cewa za su ci gaba da shirin tsige gwamnan tare da mataimakinsa.
Sun gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa rawar da ya taka na sulhu da ƙoƙarin sasanta ɓangarorin da ke rikicin, amma suka zargi Gwamna Fubara da taurin kai da rashin nuna alamar janyewa daga matsayinsa.
Mambobin majalisar, ciki har da mambobi huɗu da a baya suka nuna nadama tare da neman a dakatar da matakin, sun ce har yanzu gwamnan bai bayar da wani dalili da zai sa su janye daga shirin tsige shi ba.
Majalisar ta jaddada cewa za ta bi doka da ƙa’idojin kundin tsarin mulki wajen aiwatar da dukkan matakan da suka dace, tana mai cewa burinta shi ne dawo da daidaito da kwanciyar hankali a harkokin mulki na jihar.














